An kwantar da Mandela a asibiti
March 28, 2013Shugaban kasar Afrika ta Kudu JAcob Zuma wanda ya tabbatar da kwantar da Mr. Mandela a asibiti ya ce an kai shi ne da tsakar daren jiya Laraba sai dai shugaban bai bayyana asibitin da aka kwantar da Mandelan ba.
Da ya ke karin haske game da rashin lafiyar ta Mandela, kakakin shugaban kasar ta Afrika ta Kudu Mac Maharaj ya ce likitoci na duba tsohon shugaban kuma su na kokarin tabbatar da cewar ya samu kulawa ta musamman.
Mr. Mahraj ya kuma kara da cewar shugaba Zuma ya yi masa fatan samun lafiya cikin kankanin loakci kana ya na da da tabbacin cewar likitocin da ke kansa za su yi aiki sosai wajen tabbatar da cewar ya samu lafiya.
A dan tsakanin nan dai tsohon shugaban na kasar Afrika ta Kudu dan shekaru 94 da haihuwa ya yi ta fama da larurori musamman ma dai na cutar huhu wanda ta sanya shi kwanciya a asibiti cikin watan Disambar shekarar da ta gabata inda aka yi masa maganin cutar ta huhu baya ga wata kwarya-kwarya tiyata da aka yi masa.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Usman Shehu Usman