1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kwantar da shugaban ƙasar Irak asibiti

February 26, 2007

A yayin da rikici ke ci gaba da ƙamari a ƙasar Irak, an kwantar da shugaban ƙasa Jallal Talabani a wata assibitin ƙurraru da ke Aman na ƙasar Jordan.

Rahotanin farko da su ka bayyana wannan rashin lahia, sun nunar da cewa, Talabani ya kwanta a sakamakon bugun zucia, to amma ɗan sa Qubad Talabani, ya mussanta wannan labari.

A cewar Qubad uban sa na fama da mattuƙar gajiya ta la´akari da ayyukan da, ba dare ba ra da ya duƙufa kan su.

Kazalika opishin shugaban ya tabatar da cewa Talabani a halinda ake ciki ya fara samun sauki, an kai shi kasar Jordan dalili da karancin magani a irak.

A lokacin da shugaban ƙasa ke cikin jiya, su kuwa yan ƙunar baƙin wake, na cigaba da kai hare-kare babu ƙaƙƙabtawa a sassa daban-daban na kasa.