1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kwaso rukunin farkon 'yan Najeriya daga Sudan

May 4, 2023

Rukunin farko na 'yan Najeriya da aka kwaso su daga Sudan da ke fama da rikici, sun isa gida bayan kwashe kwanaki suna makale a cikin Sahara da kuma iyakar kasar Masar.

Hoto: ATTILA KISBENEDEK/AFP/Getty Images

Ministar jin kai ta kasar, Sadiya Umar ta ce kimanin dalibai 370 ne suka isa babban birnin kasar Abuja daga Masar. A jawabinta yayin tarbarsu a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe, Sadiya ta ce, sun yi matukar farin ciki kan yadda babu asarar rayuka a cikin 'yan Najeriya duk da irin tashin hankali da kuma wahalhalu da suka fuskanta.

Hukumomin sun ce, tun a ranar lahadin da ta gabata ne dai jiragen soji da kuma na wasu kamfanoni na Najeriya suka isa birnin Aswan na kasar Masar, sai dai an samu tsaikon kwaso daliban ne sakamakon wasu ka'idoji, wanda sai a jiyar Laraba aka warware su.

Rahotannin sun yi nuni da cewa, akwai sauran 'yan Najeriya kimanin dubu biyu da suka rage a Sudan, wanda ake sa ran kwaso su nan da kwanaki kadan.