1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An mutu a artabun 'yan kato-da-gora da 'yan ta'adda a Nijar

Salissou Boukari MA
November 4, 2021

Wasu mayakan sa kai a yankin Tillabery na Jamhuriyar Nijar, sun yi wani artabu da 'yan ta’adda bayan da suka yi musu kwanton bauna inda aka rasa rayuka da dama.

Bewaffnete Bewohner Patrouille Boko Haram Nigeria Chibok
Mayakan sa kai cikin damarar zuwa aikin kare al'umominsuHoto: picture-alliance/AP Photo/S.Alamba

A yankin Tillabery na Jamhuriyar Nijar inda rikicin ta’addanci ya yi kamari, an samu bullar ‘yan kato-da-gora masu aikin sa kai da suka hada da mutanen garuruwan da tashin hankalin ya shafa domin kawo tasu gudummawa a yakin da ake yi da yan ta’adda. Su dai wadannan mayakan sa kans un kai kibanin mutun 82 da suka soma sintiri bisa babuwa 42 dauke da makammai kuma cikinsu har da magajin garin Banibangou da mai garin Garbey da ake kira Cheik.

Sai dai wata majiya ta jami’an tsaron yankin na banibangou mai iyaka da kasar Mali ta ce mayakan sa kan na yankin Banibangou sun kai har garin Adabdab da ke a nisan km kusan 60 a arewacin garin Banibangou to cikin haka ne wani da ke bai wa ‘yan ta’addan labari ya sanar da su kasancewar mayakan sa kan a wannan yanki inda su kuma ‘yan ta’addan suka yi musu kwanton bauna suka buda wuta tsakaninsu hakan ta sanya aka samu mutuwar mutane masu yawa daga bangarorin biyu.

Hoto: picture-alliance/dpa/Stringer

Daga cikin Babura 42, guda shida ne kawai suka koma garin Dinara da mutum 15 daga cikin 84 da suka je farautar ‘yan ta’addan. Sai dai wannan lamari a cewar Hama Oumarou dan kungiyar farar hulla na jihar Tillabery, tura ce ta kai wadannan mutane ga bango har suke neman kare kansu.

 

Wannan lamari na masu aikin sa kai a jihar ta Tllabery, ya janyo martani daga masu sharhi kan harkokin tsaro, inda suke ganin cewa dan hakin da kake rainawa shi ne ke tsone maka ido. A cewar Alkassoum Abdourahamane, mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin Sahel da Afirka lamarin na bukatar taka tsantsan daga gwamnati.

Za a iya cewa dai da alama masu wannan aiki na yakin sa kai suna da cikakken goyon baya, domin kuwa a cikin su har da magajin garin Banibangou da ma hakimin Garbey, kuma wani rahoto da ake kyautata zaton na jami’an tsaro ne, ya ce daga bisani mayakan sa kan sun sake shiri domin komawa fagen daga amma kuma tare da rakiyar sojoji. Sai dai kuma da dama ne ke ganin cewa ko ba komai su mayakan sa kan zasu iya taimakawa domin mutane ne yan yankin da suka san duk wani dan yankin da ke da hannu cikin lamarin na ta’addanci.