An naɗa firimiyan Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya
March 27, 2013Jagoran kifara da gwamnati a jamhuriyar Afirka ta tsakiya, ya naɗa Nicolas Tiangaye a matsayin firamim minista. Tiangaye wanda dama can 'yan tawayen suka bada shi ga toɓeɓɓen shugaba Bozize, da ya zama firayim minista a wata gwamnati haɗaka da bata kai ko'ina ba, yace sabon shugaban ya amince masa da ya ci gaba da muƙaminsa ƙarƙashin sabuwar gwamnati. Micheal Jotodia, jagoran yan tawaye da suka karɓi iko ranar Lahdi da ta gabata, wanda ya ayyana kansa a matsayin shugaban ƙasa, yace zai yi aiki tare da Tiangaye a matsayin firayim minista.
Rohotanni dai su bayyana cewa, tun bayan wannan juyin mulki, mazaunan birnin Bangui babban birnin ƙasar musamman 'yan zamna gari banza, suke ci gaba da wasoson ganima.Tuni sun wawashe da dama daga shaguna da kuma gidajen wasu masu hannu da shuni. Sojojin Seleka sun yi yunkurin magance kwasar ganima, to amma har yanzu ba su cimma nasara ba, inji Patrice Zemoniaka wani dan jarida dake zaune a birnin Bangui.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Mohammed Nasir Awal