1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An naɗa Lagarde 'yar ƙasar Faransa sabuwar shugabar asusun IMF

June 29, 2011

A karon farko a cikin tarihi Asusun Lamuni na Duniya IMF zai kasance ƙarƙashin jagorancin mace, inda aka zaɓi Christine Lagarde 'yar ƙasar Faransa sabuwar shugabar asusun

Sabuwar shugabar Asusun IMF Christine LagardeHoto: dapd

Tuni dai ƙasashen Turai suka yi lale maraba da zaɓin na Christine Lagarde a muƙamin sabuwar shugabar Asusun Lamuni na duniya IMF. Ofishin shugaban Faransa Nikolas Sarkozy ya bayyana zaɓan ministar kuɗin ƙasar a wannan muƙamin da cewa babbar nasara ce ga Faransa. Shi ma ministan kuɗin Jamus Wolfgang Schäuble ya bayyana naɗin na ta da cewa kyakkyawan zaɓi ne, yayin da shugaban hukumar ƙungiyar tarayyar Turai Jose Manuel Barroso ya ce an yi zaɓi mai kyau.

Christine Lagarde wadda ta tsaya takara da nufin zama lambawan, yanzu dai ta kasance mace ta farko a muƙamin shugabancin Asusun Lamuni na ƙasa da ƙasa, inda za ta maye gurbin ɗan ƙasarta, Dominique Strauss-Kahn wanda yayi murabus sakamakon zargin da ake masa na yiwa wata mai shara a wani otel dake birnin New York fyaɗe.

Ta yi ta kai gwauro da mari a makonnin da suka gabata musamman a nahiyoyin Afirka da Asiya inda Lagarde mai shekaru 55 da haihuwa ta gamsar da ƙasashen, wajen ba su tabbacin cewa a gaba ƙasashe masu tasowa za su samu kyakkyawan wakilci a cikin Asusun. A jawaban da ta yi ta yi na neman goyon baya, ministar kuɗin ta Faransa ta yi ta nanata cewa.

Dominique Strauss-Kahn tsofon shugaban Asusun IMFHoto: AP

"Ni ba 'yar takarar Turai ba ce. Ba Turai na tsaya wa takara ba. Kuma ba Faransa na tsaya wa takara ba. Ni 'yar takarar dukkan ƙasashe 187 ne membobin asusun."

Christine Lagarde dai ta kasance mace ta farko da ta jagoranci ma'aikatar kuɗi da tattalin arziki a birnin Paris wato mace ministar kuɗi ta farko a jerin ƙasashen kungiyar G-8 mafiya ƙarfin tattalin arziki a duniya.

Kawo yanzu ya zama wata al'ada ɗan nahiyar Turai ya jagoranci asusun na IMF. A matsayin 'yar takara daga Turai Lagarde ta samu goyon baya ba ma daga ƙasashen Turai kaɗai ba har ma daga ɓangaren ƙungiyar haɗin kan tattalin arziki da ci-gaba wato OECD. Ga ƙasar Amirka ma Lagarde ta kasance mutum da ake maraba da ita kasancewar tana da alaƙa da Amirka domin a birnin Washimgton ta kammala jami'a kuma ta samu ƙwarewa a fannin siyasa sakamakon aikin da ta yi a ofishin wakilin jam'iyar Republican Willaim Cohen wanda ya taɓa riƙe muƙamin sakataren tsaro ƙarƙashin gwamnatin Bill Clinton.

Christine Lagarde da ministan kuɗin Jamus Wolfgang SchäubleHoto: AP

To sai dai ita ma aikin ta na da 'yar tangarɗa. Alal misali a matsayinta na minista, a shekarar 2007 lokacin da ta yanke shawarar dakatar da wata shari'a tsakanin tsohon bankin ba da rance na ƙasa wato Credit Lyonnias da kamfanin Bernard Tapie, an ba wa kamfanin diyyar Euro miliyan 285.

"A dangane da batun na kamfanin Tapie har yanzu ana cikin bincike. A cikin demokraɗiyya muke. Ko shakka babu ina son ganin an kawo ƙarshen wannan lamarin. Na yarda da wannan shari'a domin na san ban aikata wani ba daidai ba."

A ranar takwas ga watan Yuli ma'aikatar shari'a ta Faransa za ta yanke hukunci ko a gurfanar da Lagarde a gaban kuliya.

Mawallafi: Mohammed Nasiru Awal

Edita: Ahmad Tijani Lawal