An nada mace gwamnar babban bankin kasar Siriya
December 31, 2024Kafin nadinta a matsayin gwamnar babban banki ta kasance mataimakiya ta farko na gwamnan babban bankin tun hskeara ta 2018, kuma tana cikin daraktatocin hukumomin kudi na kasar. Ita dai Maysa Sabreen tana da kwarewa kan tattalin arziki.
Karin Bayani: Ko sabbin shugabanin Siriya za su yi dimukaradiyya?
A wannan Talata jirgin saman yaki na Faransa ya kai farmaki kan mayakan IS masu kaifin kishin addinin Islama a cikin kasar Siriya, kuma farmaki na farko, tun bayan kawo karshen gwamnatin Bashar al-Assad. Ministan tsaron Faransa Sebastien Lecornu ya tabbatar da haka lokacin da ya kai ziyara wa dakarun kasarsa da ke cikin dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a kasar Lebanon.
Mayakan kungiyar IS suna cikin kungiyoyin da galibin manyan kasashen duniya ke dauka a matsayin 'yan ta'adda. Kuma Fransa ta kai farmaki domin tabbatar da karya duk wani tasirin da suke da shi a yankin da suke a kasar ta Siriya. Mayakan 'yan Sunna suka jagoranci farmakin da ya kawo karshen gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad a kasar ta Siriya a farko wannan wata na Disamba.