An nada saban Praminista a Guine Bissao
November 2, 2005Talla
Shugaban kasar Guine Bissao Joao Bernardo Vierra, ya nada Aristide Gomez a matsayin saban Praminista , bayan da ya tube Karlos Gomes Junior, shugaban jami´yar PAIGI daga wannan mukami ranar assabar da ta wuce.
Jim kadan bayan wannan nadi, jam´iyar da ke da rinjaye a majalisa ta hiddo sanarwar kin amincewa da shi, ta kuma bayyana aniyar gabatar da bukatar tsige shi kansa shugaban kasar a Majalisar Dokoki.
Wannan sabuwar dambarwa za ta sake kasar Guinee Bissao a wani rikicin siyasa kawanaki kadan bayan kammala zaben shugaban kasa.