1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci gaba da takun saka tsakanin Rasha da Amirka

Suleiman Babayo
February 11, 2022

Gwamnatin Amirka da bukaci 'yan kasar fice cikin gaggawa daga Ukraine yayin da ake ci gaba da takaddama kan yuwuwar kutsen Rasha.

Ukraine Ex-Präsident Poroshenko vor Gericht
Hoto: Anna Marchenko/dpa/TASS/picture alliance

Har yanzu ba a samu wani ci gaba da ke bukata ba kan warware takaddama da ake gani tsakanin Rasha da Ukraine abin da ya kai Rasha ta jibge dakaru kusa da iyaka da kasar ta Ukraine, bayan yunkurin da aka yi na masu shiga tsakani daga Jamus da Faransa.

Tuni Shugaba Joe Biden na Amirka ya ba da umurni ga 'yan kasarsa da fice daga Ukraine nan take, amma ya ce wanna baya nuna Rasha za ta fara kuste a kasar ke nan.

Ana ci gaba da zaman rashin tabbas da yuwuwar kutse da Rasha za ta jagoranta zuwa Ukaine.