1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An nemi IMF ta yafe basuka saboda Ebola

Zainab Mohammed abubakarNovember 13, 2014

Jami'an kiwon lafiya sun bukaci Kungiyar G20 da ta taimaka wajen yakar Ebola dake ci-gaba da yaduwa a wasu kasashen yankin Yammacin Afirka

Medeor Ebola Behandlungszentrum in Liberia
Hoto: DW/J. Kanubah

Ma'aikatan kiwon lafiya sun yin kira ga shugabannin kasashe masu karfin tattalin arziki na G20, da su kara bada agaji domin shawo kan cutar Ebola mai yaduwa kamar wutar jeji a kasashen Yammacin Afirka. Jam'ian kiwon lafiya dake aiki a kasashen da cutar ta fi kamari kamar Saliyo, na ci-gaba da kokawa da hadarin dake tattare da karuwar yaduwar cutar, sakamakon rashin isassun kayayyakin kariya ga su jami'an da kuma cibiyoyin kula da lafiya.

Wata majiyar diplomasiyya na nuni da cewar, Amirka za ta yi amfani da taron na G20 wajen tursasawa hukumar bada lamuni ta duniya watau IMF, da ta soke basussukan da take bin kasashen Saliyo da Laberiya da Guinea.

Sakataren harkokin kudi na Amurka Jack Lew ya nunar da cewar, yin hakan ne kadai zai taimaka wajen gaggauta ceto kasashen daga cikin hali mawuyaci da suke ciki na yakar cutar Ebola, wadda kawo yanzu ta yi sanadiyyar rayukan mutane sama da dubu biyar.