An nuna fifiko ga siyasa a kyautar Nobel - White House
October 10, 2025
Fadar White House ta Amurka ta ce ba wa 'yar adawar Venezuela kyautar Nobel ta zaman lafiya tamkar riga malam masallaci ne kawai, domin an nuna fifiko ga siyasa ne fiye da zaman lafiya.
Fasihai 'yan Burtaniya da Faransa da Amurka sun lashe kyautar Nobel
Babban jami'in harkokin yada labaru na shugaba Donald Trump, Steven Cheung, ya ce an yi la'akari da siyasa tsagwaronta fiye da kokarin zaman lafiya a yayin bayar da kyautar ta bana da aka ba wa Maria Corina Machado, tare da bayyana shugaba Donald Trump ne wanda ya cancai samun kambun na bana.
Isra'ila da Hamas sun amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza
Steven Cheung daraktan yada labaran fadar ta Amurka, ya bayyana cewa Shugaba Trump zai ci gaba da kokarinsa na wanzar da zaman lafiya da kawo karshen yake-yaken da duniya ke fama da su don ceto rayukan al'umma.