An rantsar da sabon shugaban Ukraine
June 7, 2014
A wannan Asabar din ce aka rantsar da sabon shugaban Ukraine Petro Poroshenko. Bukin rantsar da hamshakin mai kudin kasar mai kayan kwalam na zuwa ne, a daidai lokacin da ake fatan gano bakin zaren warware rikicin siyasa da ya jagoranci sabani tsakanin Kiev da makwabciyarta Moscow.
An gudanr da bukin rantsar da Poroshenko a majalisar dokokin kasar da ke Kiev, yini guda bayan ganawarsa da shugaba Vladimir Putin, a bukin cika shekaru 70 da saukar sojojin hadin gwiwa a Faransa lokacin yakin duniya na biyu.
A bayyanarsa a gidan talabijin na Ukraine bayan ganawarsa da Putin, Poroshenko ya ce an fara tattaunawa, kuma akwai fatan warware wannan rikici ta hanya madaidaiciya. Ya kara da cewar a wannan lahadi ce, wakilan kasar ta Rasha za su je Ukraine a matsayin matakin farko na cimma warware rikicin da ke tsakanin makwabtan kasashen.
Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Umaru Aliyu