Samia Suluhu Hassan ta sha rantsuwar kama aiki a Tanzaniya
November 3, 2025
Shugaba Samia Suluhu Hassan ta kasar Tanzaniya, ta sha rantsuwar kama mulki a matsayin shugabar kasa, duk da tashin hankulan da suka biyo bayan zabenta, wanda 'yan adawa suka yi fatali tare da bayyana cewa ya yi sanadin mutuwar daruruwan mutane.
Samia Suluhu ta lashe zaben shugaban kasar Tanzaniya da kashi 97,66% na kuri'u
Rike da al' Qura'ni a hannu guda, Shugaba Hassan ta ce "na yi alkawalin yi wa 'yan kasa aiki tukuru, zan yi biyayya ga dokoki na kasa da mutunta kundin tsarin mulki." An nuna bikin rantsuwar ne duk da cewar an katse intanet a wannan kasa.
Rikicin bayan zabe a Tanzaniya ya yi kamari
Shugaba Hassan ce hukumar zabe ta kasar ta ayyana a matsayin wacce ta lashe kashi zabe da kaso 98 cikin 100 na kuri'un da aka kada, duk da yake 'yan adawa sun yi fatali da shi, suna mai cewar an yi amfani da karfin da ya wuce kima kan masu bore bayan barkewar zanga-zangar kin jinin sakamakon zaben.