1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An rantsar da shugaba Paul Biya na Kamaru a karo na takwas

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
November 6, 2025

Mr Biya mai shekaru 92, wanda ya shafe shekaru 43 yana mulkar Kamaru, shi ne shugaban kasa mafi tsufa a duniya.

Shugaba Paul Biya na Kamaru tare da mai dakinsa Chantal Biya
Hoto: Welba Yamo Pascal/AP Photo/picture alliance

Shugaba Paul Biya na Kamaru ya karbi rantsuwar jagorantar kasar a karo na 8, bayan samun nasara a zaben da aka gudanar a watan Oktoba, mai cike da rudani da tashin hankali, wanda ya janyo mutuwar masu zanga-zangar adawa da sakamakon zaben.

Mr Biya mai shekaru 92, wanda ya shafe shekaru 43 yana mulkar Kamaru, shi ne shugaban kasa mafi tsufa a duniya.

Kairn bayani:Hanyar kauce wa rikicin bayan zabe a Kamaru

An rantsar da shugaban a shagalin bikin da aka gudanar a birnin Yaounde, domin yin wa'adin shekaru 7, bayan samun kashi 53.7 cikin 100 na sakamakon zaben, yayin da babban abokin hamayyarsa Issa Tchiroma Bakary ya samu kashi 35.2 cikin 100, kamar yadda hukumar zaben kasar ta sanar.

Paul Biya shi ne shugaba na biyu da ya mulki Kamaru tun bayan samun 'yancin kai daga hannun kasar Faransa a shekarar 1960.