An rantsar da shugaban ƙasar Yuganda
May 12, 2011An gudanar da bukukuwan rantsar da sabon shugaban ƙasar Yuganda Yoweri Museveni tare da hallatar shugabannin ƙasashen Kwango, da Zimbabuwe da Najeriya da somaliya da kuma na yankin Kudancin Sudan a birnin Kampala. Museveni ɗan shekaru 70 da haifuwa zai ƙara wani sabon wa'adin mulki na shekaru biyar bayan ya ƙwaushe kusan shekaru 25 kan karagar mulki.
Shugaban dai ya na fuskantar mumunar adawa sakamakon zargin da jam'iyyun hamayya suke yi wa gwamnatin sa na cin da kuma kasa magance matsalar tsadar rayuwa .Kuma jama'a a ƙasar na kallon bai dace ba ya gudanar da shagulgulan da aka kashe maƙudan kuɗaɗe saboda taulacin da ake fama da shi kamar yadda wani ɗan ƙasar ya baiyana 'saboda inda ka duba frashin kayayakin abin masarufi a ƙasar ,abin na tayar da hankali ,kuma idan na je yin ceffane raina na ɗaɗa baci yadda kaya suka yi tsada kuma ga talauci .Shugaban dai ya yi alƙawarin ƙara farfaɗo da tattalin arikin ƙasar tare kuma da magance wahalolin tsadar rayuwa da ƙasar ke fuskanta
Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman