1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An rantsar da shugaban Senegal mafi karancin shekaru

April 2, 2024

An rantsar da Bassirou Diomaye Faye, a matsayin shugaban kasar Senegal wanda ya samu gagarumar rinjaye tun a zagayen farko na zaben shugaban kasar da aka gudanar, kwanaki akalla goma daga fitowarsa daga gidan yari.

Sabon zababben shugaban kasar Senegal Bassirou Diomaye Faye a yayin rantsuwar jan ragamar kasar
Sabon zababben shugaban kasar Senegal Bassirou Diomaye Faye a yayin rantsuwar jan ragamar kasarHoto: Zohra Bensemra/REUTERS

Shugabannnin kasashen Afrika da dama suka halarci bikin rantsuwar da aka gudanar a wani yanki da ke kusa da babban birnin kasar.  Kazalika daga bisani zai karbi mulki bayan rantsuwa a fadar shugaban kasar da ke Dakar daga hannun shugaba mai barin gado Macky Sall.

karin bayani: Senegal:Bassirou Diomaye Faye zai karbi mulki daga hannun Macky Sall

A jawabin da ya gabatar a yayin bikin rantsuwar shugaba Bassirou Diomaye Faye, ya sha alwashin yin duk mai yiwuwa wajen gudanar da mulki cikin tsoron Allah da kuma sanya muradun daukacin al'ummar Senegal gaba, tare da kira ga sauran shugabannin Afrika wajen gangamin tunkarar kalubalen tsaro a Nahiyar.

karin bayani:-  Shugaban Faransa Emmanuel Macron na son kulla alaka da sabon shugaban Senegal

Sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken ya bi sahun sauran shugabannin kasashen duniya wajen taya murna ga zababben shugaban kasar ta Senegal Bassirou Faye, tare da jaddada bukatar yaukaka dangantaka tsakanin kasashen biyu.