1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaZimbabwe

An rantsar da shugaban Zimbabuwe a wa'adi na biyu

September 4, 2023

A wannan Litinin din ce aka rantsar da Shugaba Emmerson Mnangagwa na kasar Zimbabuwe a wa'adi na biyu na mulki, bayan samun nasara a zaben kasar da ya gabata.

Shugaban Zimbabuwe, Emmerson Mnangagwa
Shugaban Zimbabuwe, Emmerson Mnangagwa Hoto: Tsvangirayi Mukwazh/AP Photo/picture alliance

Mr. Mnangagwa wanda ya yi alkawarin tsame miliyoyin 'yan kasar ta Zimbabuwe daga talauci, ya yi nasara ne a zaben ranar 23 ga watan jiya, zaben da ake tababa a kansa.

A jawabin da ya gabatar bayan shan rantsuwa a yau din, shugaban na Zimbabuwe ya bukaci hadin kan 'yan kasar tare da alkawarin sake zaburar da harkokin tattalin arziki.

Alkalin alkalan Zimbabuwe Luke Malaba da ya bayyana Shugabab Mnangagwa a matsayin wanda ya ci zabe a kotu a 2018, shi ne ya rantsar da shi a wa'adin na biyu.