1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An hari da wuka a wata Jami'a a Jamus

Abdul-raheem Hassan
June 10, 2022

Mutane hudu ne suka jikkata sakamakon hari da wuka da wani mutum ya kai a harabar jami'a Hamm-Lippstadt da ke kudancin Jamus 'yan sanda sun ce an tsare wanda ya kai hairin nan take.

Polizei-Einsatz Schule Esslingen
Hoto: Bernd Weißbrod/picture alliance/dpa

A cewar gidan rediyon WDR, wanda ya aikata laifin wani matashi ne dan garin Hamm, ya kuma afakawa dalibai ne da wuka a cikin wani dakin taron karawa juna sani a jami'ar Hamm-Lippstadt da ke North Rhine-Westphalia a kudancin Jamus.

A wani lamarin kuma, wata mata da wata yarinya ‘yar shekara bakwai sun samu munanan raunuka sakamakon hari da wuka da aka kai a wata makarantar firamare da ke Esslingen a kusa da Stuttgart.

Jamus ta kadu a farkon wannan shekarar sakamakon hare-hare a makarantu da ba kasafai ake ganin irinsu ba, bayan da wani dalibi dan shekara 18 ya bude wuta a wani dakin karatu na jami'ar Heidelberg da ke kudu maso yammacin kasar, inda ya kashe wata budurwa tare da raunata wasu uku kafin ya tsere.