1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An rufe akasarin filayen jiragen sama a Spain

December 4, 2010

Yajin aiki ya jawo cikas ga matafiya ta jiragen sama na ƙasar Spain, inda yanzu sojoji ne kawai ke kulawa da ayyukan.

Masu yajin aiki a Spain kwanan bayaHoto: AP

Gwamnatin ƙasar Spain ta miƙawa sojojin ƙasar ikon kula da sararin samaniyar ta, biyo yajin aikin da ma'aikatan suka shiga. Ma'aikatan filayen jiragen saman ƙasar, sun shiga yajin aikine tun ajiya a dai-dai lokacin da ɗimbin matafiya ke haramar tafiyar hutun ƙarshen makko, inda aka rufe filiyen jiragen saman ƙasar da yawa, ciki harda da na babban birnin ƙasar wato Madrid. Su dai ma'aikata sun bayyana cewa babu jada baya a wannan matakin da suka ɗauka, yayin da shi kuwa ministan sufurin ƙasar ya bayyana wa manema labarai cewa, wannan yajin aikin an shirya shi ne da nufin yin ɓatanci ga gwamnati mai ci. Ma'aikata dake kula da zirga zirgar jiragen saman ƙasar ta Sapain, sun jima suna tattaunawa da gwamnati kan ƙarin albashi da wasu haƙƙoki.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Zainab Muhammed Abubakar