1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An fara aikin da umurnin rufe Twitter a Najeriya

Suleiman Babayo MAB
June 5, 2021

A Najeriya kamfanonin sadarwa sun bi umurnin gwamnati wajen toshe kafar sada zumunta ta Twitter a kasar sakamakon takun saka tsakanin kafar da gwamnatin kasar.

Symbolbild | Twitter
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Skolimowska

Kamfanonin sadarwa na Najeriya sun toshe kafar sada zumunta ta Twitter a kasar, sakamakon takun saka tsakanin gwamnatin Najeriya da katafaren kamfanin na Amirka.

Tuni matakin gwamnatin Najeriya na katse shafin sada zumunta na Twitter a kasar ya bar baya da kuru inda ake ci gaba da cece-kuce tsakanin 'yan kasar. Akwai masu ganin gwamnatin ta dauki hanyar kama karya. Haka kungiyoyin rajin kare hakkin dan Adam sun soki matakin gwamnatin Najeriya kan haka. Gwamnatin ta cire sanarwar dakatar da shafin bisa zargin ana amfani da kafar wajen zagon kasa ga harkokin tsaron kasar.

Sai dai masharhanta na ganin matakin yana da nasaba da goge wani rubutun Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya da ya janyo takaddama kan yanayin tsaron da ake ciki a kasar.