1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Coronavirus na kara yin kisa a Italiya

March 5, 2020

Hukumomi a Italiya sun rufe makarantun bokon har tsawon makwanni biyu domin hana yaduwar anobar Coronavirus, Italiyar ita ce ta farko a Turai inda Coronavirus ta soma bulla. 

Italien Coronavirus Universitäten sind geschloßen
Hoto: Reuters/G. Mangiapane

Gwamnatin Italiya ta ce daga Alhamis(05-03-20) sun rufe makarantun mayan da kanana, Kawo yanzu dai cutar ta kashe mutane 107 a kasar yayin da wasu sama da dubu uku ke fama da ita. 'Yan makaranta kimanin miliyan 300 a duniya suka fasa zuwa makarantuN saboda cutar Coronavirus.