1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
IlimiAfirka

An rufe makarantun Mali

Suleiman Babayo ATB
October 27, 2025

Gwamnatin Mali ta rufe daukacin makarantun kasar saboda matsalar karancin man fetur da tsageru masu kaifin kishin addinin Islama suka haifar.

Mali Bamako 2025 | Karancin man fetur
Karancin man fetur a MaliHoto: AFP

Gwamnatin kasar Mali ta rufe daukacin makarantun da jami'oin kasar na tsawon makonni biyu daga wannan Litinin, saboda karancin man fetur da ake fuskanta a fadin kasar, bayan mayakan masu nasaba jihadi da suke da danganta da kunguyar al-Qaeda sun toshe hanyoyin shiga da man fetur zuwa cikin kasar.

Matsalolin tsaro

Karancin man fetur a MaliHoto: AFP

Ministan ilimin kasar Amadou Sy Savane ya bayyana matakin, bayan gidajen man fetur da dama sun rufe musamman a birnin Bamako fadar gwamnatin kasar.

Mayakan jihadi suna ci gaba da karfafa iko da saka matsin lamba na kassara tattalin arzikin kasar, yayin da gwamnatin mulkin sojan kasar ta gaza yin katabus. Ita dai kasar Mali da ke yankin yammacin Afirka ta shafew shekara da shekaru tana fama da matsalolin kungiyoyi masu kaifin kishin addinin Islama, wadanda suka hana kasar sakat.