An rufe oifisoshin jakadancin Amirka a Gabas ta Tsakiya
August 2, 2013Gwamnatin Amirka ta ce wannan wani mataki ne da aka dauka bisa dalilai na tsaro. Gidan telebijan CBS ya ba da rahoton da ke nuna cewa an samu labarun da ke nuni da cewa kungiyar Alka'ida na shirin kai hare-hare. Hakan kuma na da nasaba da sukan da kungiyar 'Yan uwa Musulmi ke wa sakataren harkokin wajen Amirka, John Kerry, wanda ya kira juyin mukin da sojoji suka yi wa Shugaba Mohammed Mursi tamkar sake girka demokradiya. Wani mai magana da yawon kungiyar 'Yan uwa Musulmi ya ce gwamnatin Amirka na da hannu a juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar ta Masar, inda har yanzu ake ci gaba da samun rudani. Su dai magoya bayan Mursi sun yi kira da a ci gaba da zanga-zanga.
Ministan harkokin wajen Jamus, Guido Westerwelle a yayin ziyarar da ya kai a Masar ya yi gargadi game da kara dagulewar tashin hankali.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Mohammad Nasiru Awal