An rusa kungiyar 'yan tawayen Seleka
September 13, 2013Talla
Djotodia ya bayyana hakan ne a wannan Juma'ar inda ya kara da cewar daga wannan Juma'a hadakar kungiyar ta 'yan tawaye ta daina aiki a kasar wadda tawaye da jerin juyin mulki ya tagayyara.
Wannan matakin da shugaban ya dauka dai na daga cikin yarjejeniyar da suka kulla da al'ummar kasar a baya na kau da kungiyar da ma sanya 'yan tawayen da ke cikinta su kwance damarsu ta yaki gami da sanyasu cikin rundunar sojin kasar.
Kungiyar ta 'yan tawayen ta Seleka dai wadda Michel Djotodia ke zaman mamba cikinta ita ce ta jagoranci hambarar da tsohon shugaban kasar Francois Bozize watanni shidda da suka gabata kuma ta share fagen darewa kujerar jagorancin kasar da Djotodia ya yi.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammad Nasiru Awal