An sa ranar zaben shugaban kasa a Masar
January 8, 2018Lasheen Ibrahim ya ce za a je zagaye na biyu a ranakun 24 zuwa 26 na watan Afirilu idan har bukatar hakan ta taso. A yayin ganawarsa da manema labarai Ibrahim ya ce hukumar ta shirya don karbar takardun 'yan takara daga ranar 20 zuwa 29 na watan Janairu kafin daga bisani a wallafa sunayen 'yan takarar a manyan jaridun kasar a watan Febrairu.
Wannan na zuwa ne bayan da tsohon Firaminista Ahmed Shafiq ya sanar da cewa ba zai tsaya takara a zaben shugaban kasar ba duk da cewa a farko ana ganin Shafiq mai shekaru 76 wanda tsohon kwamanda na sojojin sama ne, kana tsohon firaminista karkashin tsohon Shugaba Hosni Murabak, a matsayin wanda zai zama kalubale ga Shugaba Abdel-Fatah al-Sissi wanda ake gani zai iya sake samun shugabancin kasar ta Masar cikin sauki a wannan zaben da ke tafe.