1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An sace sama da mutane 150 a Najeriya

April 4, 2026

'Yan bindiga sun sace mutanen ne a jihar Zamfara da ke Arewa maso yammacin kasar.

An sace sama da mutane 150 a Najeriya
An sace sama da mutane 150 a NajeriyaHoto: AP/dpa/picture alliance

Jami'an tsaron Nigeriya na bin sawun ‘yan bindiga bayan da suka sace mazauna wasu ƙauyuka a yankin arewa maso yammacin jihar Zamfara, kamar yadda ‘yan sanda suka tabbatar, lamarin da ya kasance ɗaya daga cikin manyan hare-hare na baya-bayan nan a yankin.

‘Yan bindigan sun kai hari ƙauyukan Kurfa Danya da Kurfan Magaji da ke yankin Bukkuyum a ranar Alhamis, inda suka buɗe wuta kan motoci da gidaje kafin su sace mutane.

Harin ta'addanci a arewacin Najeriya ya halaka mutane 45

Shugaban ƙaramar hukumar, Umar Abubakar Faru, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa sama da mutane 150, galibi mata da yara, aka sace tare da kaisu cikin dazuzzukan da ke kewaye da yankin.

Lamarin ya tilasta wa mazauna tserewa tare da barin ƙauyukan da abin ya faru kuma ba a san inda wasu suka shiga ba.

Hatsarin kwale-kwale ya hallaka gomman mutane a Zamfara

‘Yan sandan jihar Zamfara sun tabbatar da aukuwar harin, amma sun ce har yanzu ana ci gaba da tantance adadin mutanen da aka sace.