An sace sama da mutane 60 a masallacin Juma'a a Jihar Naija
August 23, 2026
Rundunar ‘yan sandan jihar ta ce maharan sun shiga Masallacin Kpenya, da ke gundumar Dekara a karamar hukumar Borgu, da misalin karfe biyu na rana a ranar Juma’a, bayan sun kai hare-hare a kauyukan Gidan-Zana da Kpenya.
Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, Wasiu Abiodun, ya ce rahotannin farko sun nuna cewa babu wanda ya rasa ransa a harin. Ya ce an tura jami’an tsaron hadin gwiwa zuwa yankin domin tantance halin da ake ciki da kuma fara aikin ceto.
Wani mazaunin yankin ya shaida cewa harin na iya kasancewa wani shiri ne da aka tsara tun da farko, domin an kai hare-hare a lokaci guda a Dekara da wasu yankuna guda uku da ke Borgu yayin da jama’a ke gudanar da sallar Juma’a. Sai dai ba a samu damar tabbatar da wannan bayani daga wasu majiyoyi masu zaman kansu ba.
Satar mutane domin neman kudin fansa ya zama ruwan dare a wasu sassan arewa maso yamma da tsakiyar arewacin Najeriya, inda kungiyoyin ‘yan bindiga dauke da makamai ke kai hare-hare kan kauyuka, makarantu da manyan hanyoyin mota.
Hukumomi na ci gaba da aikin ceto da nemanwadanda aka sace, yayin da ake kokarin gano wadanda suka kai harin da kuma dalilin da ya sa suka kai farmakin.