An sace wani Bajamushe a birnin Kano
January 26, 2012Harkokin Tattalin Ariziki da na Rayuwar Jama'ar jihar Kano na ci gaba da samun matsala a sakamakon zaman zullumi da kuma fargaba game da sha'anin tsaro. A yanzu dai harkokin kasuwanci a birnin na Kano sun fara farfadowa, to sai dai babbar matsalar da jama'a ke fuskanta ita ce ta karancin kudi a hannuwansu sannan ga matsalar karancin man fetur ta da sake kunno kai.
Wadannan matsaloli na faruwa ne a dalilin rashin tabbas game da cikakken tsaro da kuma jita-jita dabam dabam da ake ta yadawa wadanda su suka sa bankuna da sauran wasu harkokin kasuwanci a birnin dakatar da huldodinsu da jama'a. Malam Abdulrahman Na'Abba wani manazarci ne da ya lura da yanayin rashin tabbas da jama'a ke ciki a halin yanzu.
"A halin da ake ciki babu wani tartibin abin da zaka iya gani da zai nuna maka cewa kai din nan da ka ke tafiya a kan hanya , a tsare ka ke babu abin da zai same ka. Wajen masu tsaro idan ka ce zaka je , kai ko wani labari ne da kai mai muhimmanci ba ka da hanyar da zaka samu ka sanar da su. Kai da za ka je wajensu tsoronka suke, kai kana tsoronsu su suna tsoronka, kana tafiya suna nuna maka bindiga."
Duk da yawan bankunan kasuwanci da ake da su a Kano amma 'yan kalilan ne suka bude tun daga farkon mako, su ma din ba sosai ba. Mutane da dama sun cika bankunansu don su karba ko shigar da kudi amma galibinsu ba su sami dama ba. Ga dai ta bakin wasu daga cikin dimbin mutanen irinsu Tasi'u Isma'il 'Yar da zo banki ke cewa.
"Gaskiya al'amarin dai ba ma jin dadinsa, abubuwan da suke gudana sakamakon mun fuskanci barazanar duk inda muka je bankuna sai mu tarar da mutane domin za ka iya zuwa bankuna sama da goma ko sha biyar ma ba tare da ka samu ma an bude bankunan ba .Wurin ATM ma ba a yin komai a wannan wurin." Shima Garba Muhammad Hamisu cewa ya yi "Na yi amfani da ATM dina domin su ciri kudi da zamu yi amfani da su don biyan bukata da dama, to amma kuma hakan ya ci tura. Kamar ni da nake amfani da katin UBA mun je bankuna da dama to amma ATM din ma wani a rufe zaka tarar. An rufe kofar da zaka saka katin ka. Ko da account balance dinka ba zaka iya dubawa ba ballantana ka sami damar da zaka ga kudinka ma nawa ne ko kuma ka ciri kudinka a bankin."
Ana cikin wannan hali ne sai kuma matsalar karancin man fetur ta sake kunno kai. Akasarin gidajen mai suna rufe, wadanda suke bude kuma sun cika makil da ababan hawa inda wasu daga ciki suna sayar da shi kan sabon farashi yayin da wase kuma suke sayarwa da tsada.
Mawallafi: Abdulrahman Kabir
Edita: Usman Shehu Usman