1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An sace 'yar Austria a Jamhuriyar Nijar

January 13, 2025

Matar mai shekaru 73 ta shafe shekara 28 tana rayuwa a birnin Agadez na kasar kafun a yi garkuwa da ita.

Shugaban Gwamnatin Mulkin Sojin Jamhuriyar Nijar Janar Abdourahamane Tiani
Hoto: ORTN/Télé Sahel/AFP/Getty Images

Ma'aikatar harkokin wajen Austria ta sanar da sace wata mata 'yar kasar a birnin Agadez na Jamhuriyar Nijar.

A cikin wata sanarwa da ta aike wa kamfanin dillancin labarai na AFP, ma'aikatar ta ce dole ne a tabbatar da aukuwar lamarin.

An sako Turawan da aka sace a yankin Sahel

Da farko sanarwar ta ce an shaida wa ofishin jakadancin Asutria da ke birnin Algiers na Aljeriya da Nijar ke karkashinsa batun garkuwa da matar.

Wata kafar yada labarai a Agadez mai suna Air Info ta ce sunan matar da aka sacen Eva Gretzmacher 'yar shekara 73, kuma ta shafe shekaru 28  ta na zaune a birnin na Agadez.

Faransa na zargin garkuwa da jakadanta

Hukumomin kasar ta Austria sun ce suna aiki tare da abokan hulda don sanin halin da matar ke ciki da kuma kubuto da ita.