1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Najeriya: Saka hannu kan sabuwar dokar haraji

June 26, 2025

Shugaba Bola Tinubu na Najeriya ya rattaba hannu bisa wasu dokoki guda hudu da ke zama tubalen gina kasar zuwa ga dogaro da harajin domin rayuwa da ci-gaban al'umma.

Nigeria | Shugaba Bola Tinubu na Najeriya
Shugaba Bola Tinubu na NajeriyaHoto: Sarah Meyssonnier/AP/picture alliance.com

An share tsawon wata guda tara ana tafkawa, kafin kai wa ya zuwa sabbabin dokoki guda hudu da gwamnatin Najeriya ke fatan na iya kawo sauyi cikin batun haraji a kasar. Shugaban kasar Bola Tinubu ya rattaba hannu bisa dokokin da masu mulkin ke fata na iya kai kasar zuwa kari bisa kudin shiga.

Karin Bayani:Ribar da al'umma za su mora daga dokar haraji a Najeriya 

Birnin Lagos na NajeriyaHoto: picture-alliance/dpa/A. Jallanzo

Kuma masu mulki na Abuja ba su boye ba cewar a karkashin sabon tsarin kusan biyu a cikin uku na ma'aikatan kasar sun huta da haraji. Haka kuma an cire haraji bisa masu kananan karfi a kasuwa da wuraren hidima.

Taiwo Oyedele dai na zaman shugaban kwamitin gwamnatin kasar bisa sabon tsarin haraji wanda yake ganin haka a matsayin ci-gaba da samar da hanyar tabbatar da tara kudin haraji da babu rufa-rufa.

Tashar jiragen ruwan ApapaHoto: Benson Ibeabuchi/AFP/Getty Images

A farkon shekarar badi dai ne sabbabin dokokin za su fara aiki a kasar. Dokokin kuma da majalisun kasar suka kai ga amincewa kansu bayan kai kawo a tsakanin bangarori da yawa. Sanata Sani Musa dai na zaman shugaban kwamitin kudi na majalisar dattawan tarraya Najeriya, kuma ya ce an kai ya zuwa daidaito kafin kai wa ya zuwa sabbabin dokokin.

Abujar dai ta kuma soke harajin gado da ya jawo kace nace a tsakanin gwamnatin kasar da kungiyoyin addinai.

Haka shi ma harajin mai saye zai zauna kan kaso 7.5 cikin 100, sannan kuma za a raba kudadensa kan wani tsarin da ya tanadi raba kaso 50 cikin 100 bisa tsarin daidai a tsakani na jihohin da kuma kaso 30 cikin 100 bisa yawan al'umma, ko bayan kaso 20 cikin dari na in da aka tara harajin.

To sai dai kuma ha rya zuwa yanzu yan kasar suna zaman jiran tasiri na matakai na Abujar bisa batun kudin a arayuwa da makomar miliyoyin dake dada fadawa a cikin rikici na talauci.