An saka lokacin shari'ar tsohon shugaban Masar
February 25, 2015Talla
Wata kotun ƙasar Masar ta saka ranar 16 ga watan Mayu domin yanke hukunci wa hamɓararren Shugaba Mohamed Mursi bisa zargin karya gidan fursuna. Ana zarginsa da aikata laifin lokacin boren shekara ta 2011 da ya kawo karshen gwamnatin Hosni Mubarak ta fiye da shekaru 30.
A sheakra ta 2013 ana kifar da gwamnatin Mursi inda yanzu yake fusknatar tuhuma tare da sauran mambobin ƙungiyarsa da 'yan Uwa Musulmai. Akwai kuma wani hukunci ranar 12 ga watan Afrilu da ake zargin Mursi da wasu mutane 14 da kisan masu zanga-zanga. Ƙasar ta Masar tana ci gaba da fuskantar ƙalubale na siyasa da hare-haren da ake dangantawa da masu matsanancin ra'ayi.