An sake garkuwa da wasu mutane a yankin Niger Delta
November 22, 2006Talla
Wasu yan bindiga dadi a yau laraba, da ba a san ko su wanene ba ,a yankin Niger Delta a Nigeria, sunyi garkuwa da wasu mutane da dama ciki har da wasu ma´aikatan kamfanin man kasar Italiya.
Koda yake ba a san yawan mutanen da akayi garkuwa dasun ba kawo yanzu, to amma wannan al´amari ya kasance abu na baya bayan nan aci gaba da tashin tashinar da tsagerun matasa keyi a yankin.
Ba sau daya ba sau biyu ba dai gwamnatin tarayya tasha daukar matakan dakile fitinar tsagerun matasan yankin, amma abu yaci tura, to sai dai a cewar shugaban kungiyyar MOSSOP, wato Mr Ledum Mitte, akwai gyara a ire iren matakan da gwamnati ke dauka.