1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sake kai harin kunar bakin wake a Kano

July 30, 2014

Ranar Laraba wata budurwa dauke da bom a jikinta ta kai hari a kwalejin fasaha a Kano, wanda ya zama shine hari irinsa na huu a birnin tun daga ranar Sallah tare da haddasa mutuwar mutane masu yawa

Bombenanschlag in Kaduna, Nigeria
Hoto: -/AFP/Getty Images

Zuwa yanzu mutane 3 ne akayi ittifakin sun rasa ransu a wani harin kunar bakin wake da wata budurwa ta kai harabar ofishin kwalejin fasaha ta jihar Kano wato Kano Polytechnic. An kai harin ne kan wasu dandazon daliban kwalejin da suka je domin duba sunayen garuruwna da aka tura su domin aikin bautar kasa. Wannan harin dai shine irinsa na hudu yan mata cikin Hijabi ke kaiwa a Kano tun daga ranar Sallah zuwa wannan lokaci. Wannan sabon salon harin 'yan mata ya kawo cikas matuka wajen shagulgulan Sallah a Kano.

Wannan budurwa wacce bata wuce shekaru 17 ba a duniya, ta kutsa kai ne cikin daliban da suka mayar da hankali wajen duba sunayensu a jikin allon bayanai na babban ofishin kwalejin fasaha ta jihar Kano wanda ke kan titin zuwa jami'ar Bayero, kusa da kwalejin shari'ar musulunci ta Aminu Kano, wato College for Legl Studies, ta kuma yi sa'ar tashin bam din dake makale a jikin ta wanda ya hallaka mutane 3 nan take wasu kuma da dama suka jikkata. Labaran Ibrahim Abdullah dake kan hanya lokacin da wannan bam ya fashe ya bayyana yadda ya ga dalibai da yawa sun ragargaje nan da nan kuma wurin yayi faca-faca da jini.

Shima wani ganau da ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewar sun jiyo karar fashewar wannan bam ne, kuma karar ce ma ta ja hankalinsa yayi yunkurin kawo dauki. Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano ASP Magaji Musa Majia wanda ke cikin jami'an tsaro da suka halarci wannan wuri jim kadan bayan afkuwar wannan hari, ya tabbatar da mutuwar mutane uku, harma ya ja hankalin mutane dasu zamo masu sanya idanu akan abubuwan dake faruwa a kewaye dasu.

Dalhatu Galadanci shine shugaban wannan makaranta. Ya bayyana cewar da ma dai dama an yi kokarin afakawa makarantar ne, amma ba anzo ne saboda kafe sunayen ba....

Yace ba wai saboda sunayen da aka kafe bane dama dai watakila an shiryawa kawo wa makarantar hari. Hakan ne ma yasa suka sami nasara, amma mun yi farin cikin cewar jami'an tsaro dake bakin kofa suna aikin su, shi yasa ma suka hana masu harin kusatwa cikin makarantar, shi yasa harin ya faru a bakin kofa.

Hoto: REUTERS

Sai dai kuma mutane da daman na ganin baiken hukumomin makarantar dangane da kafe sunayen a bakin kofa maimakon a cikin makaranta. Domin faruwar hare hare yasa aka girke jamain tsaro a bakin makarantu irin wadannan, dan haka duk wanda zai shiga sai an tabbatar baya dauke da wata muguwar nifaka. Hakan ne yasa aka sami nasarar afkawa daliban dake duba sunayen nasu a bakin kofa kamar dai yadda masu wannan ra'ayi ke zargi.

Mawallafi: Nasiru Salisu Zango
Edita: Umaru Aliyu