SiyasaJamus
An kashe wasu sojoji a arewacin Kamaru
July 27, 2021Talla
Wasu mahara da ba a kaiga tantace su ba, sun kashe sojojin Kamaru biyar da ma wani farar hula guda a wani hari da suka kai kan shingen binciken sojojin da ke yankin arewa mai nisa.
Jami'ai a yankin da suka tabbatar da faruwar lamarin, sun ce 'yan bindigar sun shiga wani kauye ne da ake kira Zigue a daren Talata, sannan suka tafka wannan ta'asa.
Wannan ne dai karo na biyu da ake kai hari a yankin arewan mai nisa a Kamaru, bayan wani da aka kai yankin Fotokol a karshen mako.
Kasar ta Kamaru da makwabtanta irin su Najeriya da Chadi na fama da hare-hare daga Boko Haram da ma na baya-bayan na reshen IS da ke kiran kansa ISWAP a takaice.