1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sake sace dalibai a Kudancin Kaduna

October 12, 2021

Wasu ‘yan bindiga sun kai wa makarantar horar da ilmin addinin Kirista da ke yankin kudancin kaduna hari, inda suka kwashe dalibai 5, kafin daga baya wasu ‘yan sintiri su ceto guda biyu bayan musayar wuta.

Nigeria Kaduna | Entführung Schüler Bethel Baptist School
Hoto: KEHINDE GBENGA/AFP

'Yan Bindigan dai sun kai wa makarantar hari a garin Fadan_Kaboma da kimanin karfe 8 na daren jiya Litinin, inda suka fara harbi a sama na wani tsawon lokaci kafin su kwashe daliban,

Shugaban kungiyar Kiristocin Jihar kaduna, Rev. Joseph John Hayap ya bayar ta tabbacin afkuwar wannan lamarin, inda ya nunar da cewa ‘yan bindiga sun fara tattaunawa da iyayen dalibai da suka sace, domin bukatar makudan kudade a matsayin kudin fansa

Har ya zuwa wannan lokacin dai, akwai sauran daliban makarantar Bethel Baptist High School da ‘yan bindiga suka sace tun kusan watanni 2 da suka gabata da ke hannunsu.