An sake sanya Benazir Bhutto cikin ɗaurin talala na tsawon mako guda
November 13, 2007An sake yiwa tsohuwar FM Pakistan Benazir Bhutto daurin talala a wannan karo na tsawon mako guda. Jami´an tsaro sun yiwa gidan da take a birnin Lahore na gabashin kasar, kofar rago sannan shaidu sun ce an girke ´yan sanda kimanin dubu 1 a kusa da ginin. Jami´ai a birnin Islamabad suka nunar, hukumomin Pakistan sun ba da umarnin hana Bhutto fita har tsawon kwanaki 7 don kare lafiyarta daga barazanar da ake yi na halaka ta. To amma magoya bayanta sun ce an dauki matakin ne don hana ta jagorantar wani maci da za´a yi na don nuna adawa da dokar ta baci da shugaba Pervez Musharraf ya kafa kwanaki 10 da suka wuce. A jiya daddare wani taron kasashen kungiyar Komonwelf a birnin London ya sake yin barazanar dakatar da Pakistan daga kungiyar mai membobi kasashe 53 har sai an dage dokar ta baci kafin ranar 22 ga watannan na nuwanba.