An sake tono gawarwakin 'ya'yan Mandela
July 3, 2013A yau ne aka tono gawarwakin 'ya'yan Nelson Mandela guda uku, domin sake binnesu a kauyen Qunu inda Mandela ya girma. A wannan larabar ce dai Alkalin wata kotu a kasar Afrika ta kudu, ya umurci jikan Nelson Mandela, da ya tono gawarwakin 'ya'yan shugaban gwagwarmayar launin fatar guda uku, domin mayar da su asalin inda kaburrukansu suke. Wannan dai shi ne takaddamar baya-bayannan da ya raba kawuwan iyalan na Mandela da a yanzu haka yake matsanancin hali na jinya a asibitin Pretoria. Alkali kotun yanki a Mthatha, Lusindiso Pakade, ya bukaci Mandla Mandela mai shekaru 39 da haihuwa, wanda kuma shi ne shugaban zuri'ar Mandela a hukumance, da ya daraja wa umurnin na Kotu. Tun shekaru biyu da suka gabata ne dai Mandla ya mayar da gawarwakin zuwa kauyen Mvezo mai tazarar km 20 daga gabashin Cape, inda kuma aka haifi Nelson Mandela.
Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Mouhamadou Auwal Balarabe