1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An sake zaben Ramaphosa a matsayin shugaban Afirka ta Kudu

June 15, 2024

An sake zaben Cyril Ramaphosa a matsayin shugaban kasa a zaman farko da sabuwar zababbiyar majalisar dokokin Afirka ta Kudu ta yi da yammacin ranar Juma'a 14.06.2024.

Südafrika Johannesburg | Cyril Ramaphosa,
Hoto: Zhang Yudong/Xinhua/picture alliance

Sabuwar majalisar dokokin Afirka ta Kudu ta sake zaben Cyril Ramaphosa a matsayin shugaban kasa, bayan da jam'iyyarsa ta ANC ta cimma yarjejeniyar da ba a taba ganin irinta ba a gwamnatin kasar da babbar jam'iyyar adawa ta Liberal DA.

Tuni ma a Asabar din nan kasashen Amurka da China da Ukraine da Rasha da Zimbabwe mai makwabtaka da kuma Hukumar Tarayyar Turai suka taya Mista Ramaphosa murnar samun sabon wa'adin mulki bayan da ya samu kuri'u 283 a zaben da majalisa ta yi a jiya Juma'a inda ya sha gaban Julius Malema na jam'iyyar EFF mai ra'ayin rikau wanda ya samu kuri'u 44.

Karin bayani: Kotun tsarin mulkin Afrika ta Kudu ta soke takarar Zuma

A ranar Laraba mai zuwa ne ake sa ran za a yi bikin rantsar da shugaban mai shekaru 71 a birnin Pretoria, kamar yadda wata majiya mai kusanci da gwamnati kasar ta bayyana.

 

Karin bayani: Babbar jam'iyyar adawar Afirka ta Kudu ta amince da marawa shugaba Cyril Ramaphosa

Za a dai kafa gwamnati mai zuwa ne a tsakanin jam'iyyar ANC ta Ramaphosa wadda ta samu kujeru 159 daga cikin 400 na majalisar dokoki, da kuma jam'iyyar Liberal DA mai kujeru 87 sai kuma jam'iyyar 'yan kabilar Zulu ta kasar IFP mai kujeru 17.