An saki Faransawan da aka sace a Nijar
October 29, 2013Talla
Da ya ke magana wa manema labarai a kasar Silovakiya inda ya ke wata ziyarar aiki, Hollande ya jinjinawa shugaban Nijar Mouhamadou Issoufou, saboda rawar da ya taka wajen sakinsu da aka yi.
Mr. Hollande ya kuma ce yanzu haka ministan harkokin wajen Faransa Laurent Fabius da takwaransa na tsaro Jean-Yves Le Drian, na kan hanyarsu ta zuwa kasar Nijar, domin dawo da mutanen gida Faransa, nan ba da dadewa ba inda a sada su da iyalansu.
An kame Fransawan hudu ne a ranar goma ga watan Satumbar shekara ta 2010, lokacin da suke yi wa kamfanin hakar karfen Uranium din nan na Areva mallakar kasar ta Farnsa aiki a yakin Arlit da ke arewacin Jamhuriya ta Nijar.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Usman Shehu Usman