1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An saki jagoran adawar Tanzaniya, Freeman Mbowe

November 23, 2024

An saki madugun adawan Tanzaniya, Freeman Mbowe bayan daure shi kwanaki kadan gabanin a gudanar da zaben kananan hukumomi a kasar.

Jagoran adawar Tanzaniya, Freeman Mbowe
Jagoran adawar Tanzaniya, Freeman MboweHoto: Ericky Boniphace/DW

A ranar Juma'a ne dai 'yan sanda suka kama jagoran adawar Tanzaniya, Freeman Mbowe tare wasu jiga-jigan jam'iyyarsa bayan jami'an sun tarwatsa wani taron 'yan adawa da hayaki mai sa hawaye a kudancin kasar.

A cikin sanarwar da ya fitar bayan ya shaki iskar 'yanci, Mbowe ya ce 'yan sanda sun yiwa wasu mambobin jam'iyyarsa ta Chadema dukan tashi ki sha gishiri, duk da cewa babu wanda ya nuna turjiya a lokacin kamen. Ya kara da cewa, 'yan sanda sun bukaci ya mika kansa a ranar 29 ga watan Nuwambar nan da muke ciki, sai dai a cewarsa zai tuntubi lauyoyinsa.

Karin bayani: Taƙaddamar siyasa a Tanzaniya.

Tun da farko jam'iyyar Chadema ta 'yan adawar ta yi zanga-zanga a farkon wannan makon, don nuna rashin amincewa da matakin rashin adalci da aka yi wa wasu 'yan takararta gabanin zaben yankuna, wadanda aka soke sunayensu. Zaben ranar 27 ga watan Nuwambar shekarar 2024 zai kasance wani babban tsauni a siyance kafin babban zaben kasar da zai gudana a watan octoban badi.