An saki Tandja Mamadou
May 10, 2011![](https://static.dw.com/image/4537223_800.webp)
Talla
Rahotanni daga birnin Yamai fadar mulkin jamhuriyar Nijer sun nuna cewar kotun ɗaukaka ƙara ta saki tsofon shugaban ƙasar Tandja Mamadou bayan da ya share sama da watanni goma a tsare tun bayan kifar da gwamnatin sa da sojoji suka yi a ranar sha takwas ga watan fabarairu na shekara ta 2010 a sakamakon rikicin siyasar da ya biyo bayan shirinsa na ta zarce. Ga dai ƙarin rahotanni daga wakilanmu a birnin Yamai Gazali Abdu Tasaoua da Mamman Kanta. Sai kuma hira da Yahouza Sadissou Madobi yayi tare da Dr. El-Back Adam, malami a jami'ar Yamai akan sakin na Tandja Mamadou.
Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal
Edita: Zainab Mohammed Abubakar