An saki wadda ta mari sojan Isra'ila
July 29, 2018Talla
Jami'ai a Isra'ila, sun saki yarinyar nan 'yar falasdinawa Ahed Tamimi, wadda aka tsare a bara bayan wani faifan bidiyo ya nuno ta, tana marin wani sojan kasar a gabar yamma ta kogin Jordan.
Ita dai yarinyar mai shekaru 17 da haihuwa, ta zama wata jaruma a idon falasdinawa bayan sauke fushinta da ta yi kan sojin na Isra'ila da suka shige masu gida.
Hukumomin gidan yarin yankin ne suka tabbatar da sakin Ahed Tamimi.
Cikin watan Disambar bara ne dai aka tsare ta, tare da mahaifiyarta, wadanda yanzu ke hannun sojojin na Isra'ila.
Isra'ilawa a nasu bangaren sun yaba wa sojan da yarinyar ta mara, saboda kai zuciya nesa da ya yi duk da girman laifin da ta aikata a dokar kasar.