1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

An sako karin daliban Kaduna a Najeriya

September 27, 2021

An sako wasu daga cikin daliban makaranta da aka sace watanni biyu da suka gabata a jihar Kaduna da ke a arewacin Najeriya, bayan sake biyan kudaden fansa.

Nigeria | Schulkindern entführt
Hoto: AP/picture alliance

'Yan bindiga a Najeriya, sun sako karin wasu dalibai daga cikin dalibai sama da 100 da suka kwashe a makarantar Bethel Baptist High School ta Kaduna a farkon watan Yulin bana.

Rahotanni sun ce dalibai 10 ne suka sako a ranar Lahadi, bayan biya kudin fansa a cewar kungiyar iyaye da malamai ta makarantar.

Sace daliban makarantar ta Bethel dai, ya kasance cikin manyan sace-sacen jama'a musamman 'yan makaranta da ake fama da su a yankin arewa maso yammacin Najeriya.

'Yan bindigar na sakin daliban ne rukuni-rukuni, abin da shugaban kungiyar Kiristan kasar reshen jihar Kaduna, Rev. Joseph John Hayab, ya ce 'yan bindigar na yin hakan ne domin tabbatar da samun kudade daga iyayen yaran.

Rev. Hayab ya ce dalibai 11 ne suka rage a hannun masu garkuwar, yana mai kyautata fatan samun su a nan gaba.