An sako wani ɗan ƙasar Jamus da aka sace a Najeriya
October 30, 2014Talla
An ba da rahoton cewar wani ɗan ƙasar Jamus wanda wasu 'yan bindiga suka sace a makon jiya a jihar Ogun a yankin kudu maso yammacin Najeriya an sakoshi.
Kamfanin Julius Berger wanda a nan mutumin yake aiki ya sanar da cewar an sako ma'aikacin nasa salin alin. Sai dai kuma kamfanin mai yin aikin gine-gine a Najeriya bai bayar da arin haske ba a game da yadda aka ako mutumin.