SiyasaJamus
An sako wasu daliban Kaduna a Najeriya
September 19, 2021Talla
Shugaban kungiyar mabiya addinin Kirista a Najeriya CAN reshen jihar Kaduna, Reverend John Joseph Hayab, wanda ya tabbatar da sakin daliban, ya ce har yanzu da sauran dalibai 21 da masu garkuwar ke rike da su.
Reverend Hayab, ya ce an biya kudin fansa kafin a kai ga sakin takwas daga cikin daliban, yayin kuma da aka saki biyu daga cikin su saboda yanayi rashin lafiya da suke ciki.
Ko a watan jiya ma dai, masu garkuwar sun sako yara 15 daga cikin daliban, bayan sakin wasu 28 cikin watan Yuli.
Kimanin daliban na Bethel Baptist 150 ne 'yan bindigar suka kwashe cikin watan na Yuli.
Reverend John Hayab, ya ce kudi ne suke nema ya sa suke sakin daliban rukuni-rukuni.