An sako wasu 'yan matan Dapchi
March 21, 2018Talla
Mayakan kungiyar Boko Haram sun maido da yawancin 'yan mata 110 da suka sace a makarantar kwana ta 'yan mata da ke Dapchi jihar Yobe a watan da ya gabata, tare da yin gargadi da kakkausar murya, a cewar wadanda suka ganewa idanunsu.
Rahotanni sun ce da misalin karfe biyu na tsakar dare ne, mayakan suka shiga cikin tsakiyar garin na Dapchin da mayan motoci guda tara dauke da 'yan matan. A daidai lokacin da mazauna garin suka fito cikin firgici, 'yan Boko Haram din sun yi gargadin ga iyaye na kada su sake tura 'ya'yansu mata makaranta.
A ta bakin minisatn yada labaran Najeriya Lai Mohammed, gwamnati bata biya komai kafin sakin 'yan matan ba, sai dai masu sharhi a fannin tsaro na cewa hakan abu ne mai kamar wuya.