An sallami Boris Johnson
April 12, 2020Talla
Mr. Boris Johnson dai ya yi jinyar cutar ne na mako guda kafin sallamo shi da aka yi a yau Lahadi, sai dai babu kuma labarin komawarsa aiki nan take.
Tun a karshen watan jiya ne kuwa ya sanar da killace kansa bayan ya kamu da matsalar.
An dai sha zargin Firamnistan na Birtaniya da jan kafa tun da fari, wajen daukar tsauraran matakai a kan cutar, musamman ma lokacin ta fara bayyana a kasar cikin watan Fabrairu.
Sama da mutum dubu 10 ne dai wannan annoba ta kashe a Birtaniyar, kamar yadda alkaluman hukumomi suka tabbatar a yau.