SiyasaJamus
Umaro Sissoco Embalo ya sallami firaministansa
August 7, 2025
Talla
Kawo yanzu, ba a san dalilan korar mista Barros ba, mamba na jam'iyyar African Party for Independence of Guinea mai cike da tarihi.
wanda ya dade yana adawa da shugaba Embalo wanda aka nada a kan matsayin tun watan Disamba na shekara ta 2023.
Korar tasa na zuwa ne, watanni hudu gabanin zaben shugaban kasa da shugaba Embalo ya tsayar a ranar 23 ga watan Nuwamba,
biyo bayan rikicin siyasa da aka shafe watanni da dama ana alakanta shi da ranar da wa'adinsa zai kare.