Shugaban Brazil ya samu sauki
January 5, 2022Talla
A wannan Laraba Shugaba Jair Bolsonaro na kasar Brazil ya ce an sallame shi daga asibiti bayan da aka yi masa jinya kan cutar da ta same shi a hanji. Tun lokacin yakin neman zaben shekara ta 2018 aka soke shi da wuka yayin gangamin yakin neman zabe.
Dan shekaru 66 da haihuwa shugaban ya bayyana sallamar daga asibiti a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na zamani, tare da wallafa hotonsa da na likitocin da suke kewaye da shi a wani asibitin birnin Sao Paulo na kasar ta Brazil.