An sallami Fafaroma daga asibitin Italiya
April 1, 2023
Talla
An sallamo shugaban Kiristocin duniya mabiya darikar Katolika Fafaroma Francis daga asibiti bayan jinyar ciwo mai nasaba da numfashi.
A yayin tattaunawarsa da manema labarai ta wannan Asabar, Fafaroma ya ce zai halarci dandalin Saint Peters Square domin jagorantar taron ibadar da aka saba yi a duk shekara.
Da farko dai mabiya sun nuna damuwa tare da fargabar shugaban na Katolika ba zai samu sukunin jagorantar ibadun Ista da za a yi a wannan wata na Afrilu ba. To amma Fafaroma mai shekaru 86 ya ce tun a ranar Laraba ya fara samun saukin jikinsa, inda ma ya yi amfani da damar wajen jinjina wa malaman asibiti da ya ce sun nuna jarumta wajen samar da waraka.